Abdul Saboor

Kudu da Tsakiyar Asiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 3

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan uku don bayanai kan Abdul Saboor. Saboor ƙwararre ne wajen haɗa bama-bamai kuma abokin harkar ƙungiyar Hezb-e Islami Gulbuddin (HIG). Shi ne ke da alhakin kai harin bam a cikin mota a birnin Kabul na Afghanistan ranar 16 ga Mayun 2013. Harin ya kashe sojoji biyu da kuma ‘yan kwangila huɗu duka Amurkawa. Fashewar ta kuma kashe ‘yan Afghanistan takwas – ciki har da yara biyu, ya raunata wasu 37, sannan ya tarwatsa wata motar sojan Amurka mai silke.

Saboor da ƙwararren mai haɗa bam na HIG, Abdullah Nowbahar, suna cikin manyan waɗanda suka kai harin bam kan wata motar bas da ke ɗauke da ma’aikata ‘yan ƙasar waje na Filin Jirgin Sama na Kabul ranar 18 ga watan Satumban 2012. Fashewar ta kashe mutum 12.

A ranar 10 ga watan Maris na 2016, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Saboor a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Saboor taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Saboor.

Skip to content