Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don samun bayanai kan Ali Atwa, wanda kuma aka sani da Ammar Mansour Bouslim da Hassan Rostom Salim. Atwa da ake zargin mamban Hizballah ne, ana neman sa ne saboda rawar da ya taka garkuwa da jirgin saman a TWA Flight 847 a 1985.
A ranar 14 ga Yunin 1985, ‘yan ta’adda suka karkatar da jirgin saman na TWA Flight 847 daga Athens zuwa Rome. Tsawon kwana 17 aka tilasta wa jirgin ya yi ta shawagi a saman Tekun Mediterranean ɗauke da fasinjoji 153 da ma’aikata daga Beirut zuwa Algiers, inda ya yi ta yin hakan kuma ya sauka Beirut har sau uku. A tsayawarsa ta farko a Beirut, masu garkuwar suka dinga dukan wani sojan Amurka Robert Stethem, sannan daga baya suka harbe shi.
A ranar 14 ga Nuwamban 1985, an gano laifin Atwa sakamakon rawar da ya taka a garkuwa da jirgin. A ranar 12 ga Oktoban 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Atwa a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Atwa taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Atwa. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. Atwa na cikin jerin sunanyen ‘yan ta’adda da FBI ta fi nema. An yi imanin cewa yana Lebanon.
