Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 3 don bayanai kan Ahmed Iman Ali. Ali shahararren kwamanda al-Shabaab ne, Amurka ta ayyana matayi ta Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ko kuma Foreign Terrorist Organization (FTO), wanda kuma ya yi aiki a matsayin shugaban ƙungiyar a Kenya a 2012. Ya jagoranci ayyukan ƙungiyar wajen kai wa Kenya hare-hare, ciki har da hari kan Dakarun Kenya a Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka na African Union Mission a Somalia (AMISOM). Ɗaya daga cikin hare-haren a 2016 a El Adde, Somalia, ya lalata baki ɗayan sansani soja sannan ya kashe fiye da sojojin Kenya 140.
Ali ne kuma yake da alhakin yaɗa farfagandar al-Shabaab kan gwamnatin Kenya da fararen hularta, kamar bidiyon da ya fitar a Yulin 2017 yana gargaɗin Musulmai da ke cikin rundunar sojan Kenya. Kazalika, Ali ya dinga ɗaukar wa al-Shabaab mayaƙa, inda ya dinga neman matasa marasa hali a Nairobi, kuma ya tara wa al-Shabaab kuɗaɗe daga masallatai.
A ranar 8 ga Maris na 2018, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana Ali a matsayin Ɗan Ta’addan na Duniya ƙarƙashin Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Ali taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Ali. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa al-Shabaab kayan aiki da gangan.
