Ahmad Ibrahim al-Mughassil

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don bayanai kan Ahmad Ibrahim al-Mughassil, wanda kuma aka sani da Abu Omran. Al-Mughassil wanda ake zargin shi ne shugaban ɓangaren soja na Ƙungiyar Hizballah a Saudiyya (Saudi Hizballah) ta ta’addanci, ana neman sa saboda rawar da ya taka a harin bam kan ginin Khobar Towers da ke kusa da Dhahran a Saudiyya.

A ranar 25 ga watan Yunin 1996, mambobin Hizballah a Saudiyya (Saudi Hizballah) suka tashi bam da ke jikin mota a wurin ajiye motoci na ginin Khobar Towers, wani rukunin gidaje da da sojojin Amurka ke zaune a ciki. Fashewar ta tarwatsa gini mafi kusa tare da kashe dakarun Amurka 19 da wani ɗan Saudiyya, kuma ya raunata ɗaruruwan ‘yan ƙasashe da dama.

A ranar 21 ga Yunin 2001, wani rukunin masu taimaka wa alƙali ya gano laifin al-Mughassal da wasu mutum 13 da ke da hannu a harin.

A ranar 12 ga Oktoban 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana al-Mughassil a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana al-Mughassil taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ya mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amukawa yin duk wata hulɗar kuɗi da al-Mughassil. Yana cikin jerin sunayen ‘ya ta’addan da FBI ta fi nema.

Skip to content