Adham Husayn Tabaja

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 10

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 10 don bayanai da za su kai ga daƙile harkokin kuɗi na Hizballah. Adham Husyan Tabaja, wanda aka sani kuma da Adham Tabaja, mamban Hizballah ne da ke da alaƙa ta kai-tsaye da shugabannin ƙungiyar ta ta’addanci, ciki har da yadda Islamic Jihad ke gudanar da ayyuka.

Tabaja na da kadarori a Lebanon a madadin Hizballah. Shi ne ke da hannun jari mafi girma a kamfanin gine-gine na Al-Inmaa Group for Tourism Works, wanda Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta saka wa takunkumi a Yunin 2015. Kamfanin Tabaja na Al-Inmaa Engineering and Contracting na ɗaya daga cikin kamfanonin gine-gine mafiya girma da suka yi nasara a Lebanon tun daga shekarun 1990 kuma Hizballah na amfani da shi wajen zuba jari. A 2006, Tabaja ya yi amfani da kusancinsa da shugabannin Hizballah ya gina babban kamfanin Al-Inmaa Engineering and Contracting a Dahieh da ke ƙarƙashin ikon Hizballah a Beirut da Lebanon.   A baya-bayan nan, Tabaja ya yi amfani da rassan Al-Inmaa Engineering and Contracting a Iraq don karɓar kwangilar man fetur da gine-gine da zai ba shi damar amun kuɗi da kuma haɓaka ayyukan Hizballah. Tabaja da kamfanoninsa sun kuma samu kwangiloli a yankin Green Zone na birnin Baghdad, Iraq. Tabaja ya yi aiki da shugabannin Hizballah, ciki har da jagoran siyasa Muhammad Kawtharani, saboda waɗannan ayyukan.

A ranar 10 a watan Yunin 2015, Ma’aikatar Baitul-Malin Amurka ta ayyana Tabaja a matsayin Ɗan Ta’adda na Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon hakan, baya ga sauran abubuwa, an hana Tabaja taɓa duk wata dukiya ko kadarori da ta mallaka da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kuɗi da Tabaja. Ƙari a kan haka, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya haɗa baki wajen samar wa Hizballah kayayyaki ko taimako, wadda Amurka ta ayyana Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasashen Waje. Saudiyya ma ta ayyana Tabaja da kamfanoninsa a matsayin ‘yan ta’adda.

Skip to content