Abderraouf Ben Habib Jdey

Kudu da Tsakiyar Asiya | Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya | Yammacin Duniya

Lada

Har zuwa dalar Amurka miliyan 5

Ba da gudunmawarka.

Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan 5 don neman bayanai kan Abderraouf Ben Habib Jdey, wanda kuma ake kira Farouq al-Tunisi. Jdey na da alaƙa ta kusa da mayaƙan ƙungiyar Al-Ka’ida (Al-Qa’ida – AQ) kuma yana da hannu a shirya yin garkuwa da jirage da kuma sauran ayyukan ta’addanci. Jdey abokin Faker Ben Abdelaziz Boussora (hyperlink) ne, wanda ake zargi da ta’addanci, kuma ana zargin sun taɓa yin balaguro tare.

An haifi Jdey a Tunisa a 1965. Ya yi ƙaura zuwa Montreal da ke Canada a 1991 kuma ya zama ɗan ƙasar Canada a 1995. A 1999, Jdey ya bar Canada zuwa Afghanistan, inda ya samu horo na ta’addanci da dabarun yaƙi. Ya shiga fafatawa don yaƙar Afghan Northern Alliance sannan ya rubuta wata wasiƙa yana mai bayyana aniyarsa ta yin shahada ta hanyar jihadi. A tsakanin wannan lokacin, ya fito cikin wani bidiyon shahada da aka samu a gidan jagoran AQ a 2001.

Jdey ya koma yankin Montreal a 2001. Bayan shafe lokaci tare da wasu masu tsattauran ra’ayin game da shiga jihadi, sai ya bar Canada. Hukumomi na tsoron zai iya komawa Canada ko Amurka don shirya wani hari.

Skip to content