Lada Don Adalci na ba da tayin lada da ya kai dalar Amurka miliyan biyar don bayanai kan hare-haren 2008 da aka kai a Mumbai. Tun daga farkon 26 har zuwa 29 ga watan Nuwamban 2008, wasu mutum 10 da suka samu horo daga Lashkar-e Tayyiba (leT), wata ƙungiya da Amurka ta ayyana matsayin Kungiyar Ta’addanci a Kasashen Waje, suka kai tsararrun hare-haren ta’addanci wurare da dama a Mumbai na Indiya, inda suka kashe mutum 166. An kashe Amurkawa shida yayin ƙawanyar ta kwana uku: Ben Zion Chroman, da Gavriel Holtzberg, da Sandeep Jeswani, da Alan Scherr, da Naomi Scherr, da kuma Aryeh Leibish Teitelbaum. Manyan jagororin da suka kai mummunan harin har yanzu ba a kama su ba, kuma ana ci gaba da bincike.
Kotun tarayya a Amurka ta gano David Coleman Headley da Tahawwur Rana sun taimaka wa ayyukan LeT na ta’addanci. A watan Maris na 2010, ɗan Amurka Headley ya amsa laifuka 12 da ake tuhumarsa da su bayan kama shi a Oktoban 2009. A watan Janairun 2013 aka ɗaure Headley shekara 35 a gidan yari saboda laifukan ta’addanci da ke da alaƙa da shirya hare-haren Mumbai da kuma wasu ynƙurin kai wa wani gidan jairda hari a Denmark. Rana wanda ɗan ƙasar Canada ne kuma daɗaɗɗen aboki ga Headley, an ɗaure shi shekara 14 a gidan yari saboda haɗa baki wajen taimaka wa yunƙurin kai harin ta’addanci na Denmark da kuma tallafa wa ƙungiyar LeT.
Kotun tarayya a Amurka ta gano laifukan waɗannan da ake zargi:
- Sajid Mir, wanda ya jagoranci hare-haren 2008, ya tsara da kuma aiwatar da hare-haren;
- Manjo Iqbal, mazaunin Pakistan ne kuma mai alaƙa da LeT, wanda aka shirya da kuma biyan kuɗaɗen hare-haren da LeT ta kai;
- Abu Qahafa, mazaunin Pakistan ne kuma mai alaƙa da LeT, wanda ya horara da wasu dabarun yaƙi kuma aka yi amfani da su wasu hare-hare; da
- Mazhar Iqbal, wanda aka sani da Abu al-Qama, mazaunin Pakistan ne kuma kwamandan LeT.
