Fafutikar Neman Sauya Hali (Revolutionary Struggle – RS) ta ɓullo a 2003 bayan kama mambobin ƙungiya biyu masu aƙidar Markisanci na Girka, 17 November da Revolutionary People’s Struggle. Ƙungiyar mai tsattsauran ra’ayin Markisanci, RS ta kai hare-hare kan kadarorin Girka da na Amurka a Girkar. Da farko RS ta gawurta lokacin da ta ɗauki nauyin harin ranar 5 ga Satumban 2003 a kan Kotun Athens lokacin da ake shari’ar mambobin ƙungiyar 17 Nuwamba. RS ta ɗauki alhakin makaman roka da ta harba kan ofishin jakadancin Amurka a Janairun 2007 da ke Athens da harin bam na watan Maris ɗin 2009 kan reshen bankin Citibank da ke Athens.
A ranar 18 ga Mayun 2009, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana RS a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Daga baya, a ranar 17 ga Satumban 2009, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana RSmatsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana RS taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da RS. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka da gangan wajen samar wa RS kayan aiki.
