An ƙirƙiri Jam’iyyar ‘Yanta Al’umma (Revolutionary People’s Liberation Party/Front – DHKP/C) a 1978 a Turkiyya. DHKP/Cna goyon bayan aƙidar Markisanci sannan tana adawa da Amurka da NATO da kuma ƙasar Turkiyya Kungiyar ta kai wa kadarorin Amurka hari, wanda ya hada da sojojin Amurka da jami’an difilomasiyya da cibiyoyi, jami’an NATO da cibiyoyi, da kuma buƙatun Turkiyya tun shekarun 1990. A watan Fabarairun 2013, wani jami’in DHKP/C ya tayar da bam ɗin da ke jikinsa a ofishin jakadancin Amurka da ke Ankara. Harin ya kashe wani mai gadi ɗan Turkiyya da raunata ɗan jaridar ƙasar. A watan Maris na 2013, mambobin ƙungiyar uku sun kai hari kan Ma’aikatar Shari’a da shelikwatar jam’iyyar Justice and Development Party a Ankara ta hanyar amfani da gurneti da makamin roka.
A ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana DHKP/C a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje wato Foreign Terrorist Organization bisa sashe na 219 na Dokar Kaura da Zama Dan Kasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. A ranar 31 ga Oktoban 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana DHKP/C matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana DHKP/C taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da DHKP/C.Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa DHKP/C kayan aiki da gangan.
