Ƙungiyar Haɗin Kai da Jihadi a Yammacin Afirka (Movement for Unity and Jihad in West Africa – MUJWA) ta bayyana a Yammacin Afirka a 2011 bayan ɓallewa daga kungiyar al-Qa’ida a Yankin Musulman Maghreb (Al-Qa’ida in the Islamic Maghreb – AQIM). A 2013, ƙungiyar ta haɗe da al-Mourabitoun, wadda daga nan ta shige cikin Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM).
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana JNIM a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa (wadda aka yi wa kwaskwarima) ranar 6 ga watan Satumban 2018.
