Jemaah Islamiya (JI)

Gabas da yanKin Pacific

Lada

Ba da gudunmawarka.

Jemaah Islamiya (JI) ƙungiyar ta’addanci ce a kudu maso gabashin Nahiyar Asiya da ke son kafa daular Musulunci a can.  JI ta kai hare-hare a yankin, ciki har da harin bam na Oktoban 2002 kan gidan rawa na Bali da ya kashe mutum fiye da 200, harin bam na 2003 kan otel ɗin Marriot a Jakarta da ya kashe mutum 12, da kuma harin Oktoban 2005 na ƙunar-baƙin-wake a Bali da ya kashe mutum 26.

A ranar 23 ga watan Oktoba na 2002, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ISIS-GS a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima, da kuma Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wanda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana JI taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da JI. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa JI kayan aiki da gangan.

Skip to content