Jajayen Dakarun Japan (Japanese Red Army - JRA)

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya | Turai da Eurasia

Lada

Ba da gudunmawarka.

An kafa Jajayen Dakarun Japan (Japanese Red Army – JRA) a wuraren shekarun 1970 bayan allewa daga ƙungiyar Japanese Communist League-Red Army. Babbar buƙatar JRA ita ce ta hamɓarar da gwamnatin Japan da kuma masarautar ƙasar. JRA ta ƙaddamar da hare-hare masu yawa a faɗin duniya, ciki har da harin 1972 a filin jirgin sama na Lod da ke Isra’ila da ya kashe mutum 26 tare da raunata 80, da yunƙuirin 1975 na karɓe iko da ofishin jakadancin Amurka na Kuala Lumpor, da kuma harin bam a 1988 kan gidan rawa na USO a Naples da ke Italiya, wanda ya kashe mutum biyar. An kama shugaban ƙungiyar a 2000, kuma ta sanar da yunƙurin rushe ta a 2001.

A ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana JRA a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Ranar 8 ga watan Oktoban 2001, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta janye ayyana JRA a matsayin ƙungiyar ta’addanci (FTO). 

Skip to content