Jihadin Musulunci a Masar (Egyptian Islamic Jihad – EIJ), wadda kuma ake kira al-Jihad, wata ƙungiyar masu tsattsauran ra’ayi ce a Masar wadda aka kafa a shekarun 1970. Babban muradin EIJ shi ne tumɓuke gwamnatin Masar tare da maye gurbinta da ta Musulunci. Ƙungiyar ta ƙware wajen kai wa manyan jami’an gwamnatin Masar hare-hare. Ƙarƙashin jagorancin Ayman al-Zawahiri, EIJ ta haɗe da a-Ƙa’ida a watan Yunin 2001.
