Al-Qa’ida a Zirin Ƙasashen Larabawa (Al-Qa’ida in the Arabian Peninsula – AQAP) ƙungiya mai tsattsauran ra’ayi a Yemen da ta bayyana a Janairun 2009 bayan ‘yan ta’addan Saudiyya da na Yemen sun haɗe.
Babban ƙudirin AQAP shi ne kafa daular Musulunci da kuma aiki da shari’a a ƙasashen Larabawa da yankin Gabas ta Tsakiya baki ɗaya. AQAP ta kai wa kadarorin Amurka da na ƙasashen Yamma da na cikin gida hari a ƙasashen Larabawa da sauran ƙasashe. Ƙungiyar ta ɗauki nauyin kai hare-hare da dama, ciki har da na watan Janairun 2015 da ta kai kan ofishin jaridar barkwanci ta Charlie Hebdo a Paris wanda ya kashe mutum 12.
AQAP ƙawar babbar ƙungiyar ta’addanci ta al-Qa’ida (AQ) kuma tana aiki ne tare da shugabanninta na duniya don neman mabiya a ƙasashen Yamma da kuma faɗaɗa ƙawance. Babban amfanin AQAP a wajen AQ shi ne matsayinta na dillaliya a harkokin kuɗi tsakanin abokan hulɗarta.
AQAP ta kai wani harin da bai yi nasara ba kan wani jirgin sama da bam ranar 25 ga watan Disamban 2009, wanda ɗan ta’adda Umar Farouk Abdulmutallab ya kai. Ƙungiyar ta kuma ɓoye bama-bamai a cikin magurzai (printers) da ake shirin kaiwa Amurka a cikin wasu jiragen ruwa biyu a ƙarshen shekarar 2010; an gano bamabaman kuma aka kwance su ranar 29 ga watan Oktoban 2010 yayin da aka yi zango a wuri biyu.
A ranar 19 ga watan Janairu na 2010, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQAP a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje a ƙarƙshin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa da aka yi wa kwaskwarima, da kuma ayyana ta Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224 da aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana AQAP taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadara da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin hulɗar kuɗi da AQAP. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko taimakawa wajen samar wa AQAP kayan aiki.
