Al-Qa'ida a Iraqi (Al-Qa'ida in Iraq - AQI)

Nahiyar Near East – Yammacin Afirka da Gabas ta Tsakiya

Lada

Ba da gudunmawarka.

Ƙungiyar al-Qa’ida a Iraqi (Al-Qa‘ida in Iraq – AQI), marigayi ɗan ta’adda Abu Mus’ab al-Zarƙawi ne ya kafa ta a 2004, wanda ya yi mubaya’a ga shugaban al-Qa’ida Usama bin Ladin. A shekarun 1990, al-Zarƙawi ya kafa ƙungiyar al-Tawhid wal-Jihad – wadda ta rikiɗe zuwa AQI– don yin adawa a kasancewar sojojin Amurka da ƙasashen Yamma a ƙasashen Musulmai, da kuma taimakon da ƙasashen Yamma ke bai wa Isra’ila da kafuwarta. Al-Zarƙawi ya je Iraqi lokacin yaƙin Operation Iraqi Freedom – sanda Amurka ta jagoranci ƙasashe fiye da 40 don mamaye Iraqi – sannan ya jagoranci tawagarsa a yaƙi da sojojin Amurka da ƙawayenta har zuwa mutuwarsa a Yunin 2006. AQI ta kai wa sojojin ƙawance da na Iraqi da fararen hula hare-hare don korar baƙi daga Iraqi, da rage goyon bayan da Amurka da gwamnatin Iraqi ke samu, sannan ya samu sabbin mayaƙa. A watan Oktoban 2006, AQI ta sanar da sauya sunanta zuwa Islamic State in Iraq wato Islamic State a Iraqi. Ƙungiyar ta koma Islamic State of Iraq and Syria (ISIS) wato Islamic State a Iraqida Syria (ISIS) a 2013 bayan ta nesanta kanta daga AQ.

A ranar 17 ga watan Disamban 2004, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQI (ISIS a yanzu) a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Ƙasar Waje ƙarƙashin sashe na 219 na Dokar Ƙaura da Zama Ɗan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Kafin haka, a ranar 15 ga watan Oktoba na 2004 Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana AQI matsayin Ƙungiyar Ta’addanci ta Duniya bisa Umarnin Shugaban Ƙasa na Executive Order 13224, wadda aka yi wa kwaskwarima. Sakamakon haka, an hana ISIS taɓa dukkan dukiyar da ta mallaka ko kadarori da ke ƙarƙashin ikon Amurka, sannan an haramta wa Amurkawa yin duk wata hulɗar kasuwanci da ISIS. Laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka a samar wa ISIS kayan aiki da gangan.

Skip to content