Ƙungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group – ASG) ta balle daga Ƙungiyar ‘Yanta Yankin Moro ta Ƙasa (Moro Liberation Front) a farkon shekarun 1990 kuma tana cikin kungiyoyin ta’adda mafiya muni a Philippines. Bayan tasirin da al-Ka’ida ta yi mata tun farko, ASG na yunƙurin kafa daular Musulunci a yammacin Mindanao da kuma Sulu Archipelago. A baya-bayan nan, wasu ‘yan ƙungiyar sun ƙulla mu’amula da ‘yan ISIS na yanki mai suna ISIS-Philippines. Ƙungiyar ta tafka ayyukan ta’addanci a fa ɗin ƙasar Philippines, da suka haɗa da harin bam, da kashe-kashe, garkuwa da mutane don neman ƙudin fansa.
A ranar 8 ga watan Oktoban 1997, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana ASG a matsayin ƙungiyar ta’addanci ta ƙasar waje wato Foreign Terrorist Organization (FTO) bisa sashe na 219 na Dokar Kaura da Zama Dan Ƙasa, wadda aka yi wa kwaskwarima. Daga baya kuma a ranar 23 ga watan Satumban 2001, an saka ASG a kan Umarnin Shugaban Ƙasa na Annex to Executive Order 13224. Sakamakon wannan mataki, daga cikin abubuwa, duk wata dukiya ko hannu a cikin dukiyar ta ASG da ke ƙarƙashin dokokin Amurka, an hana su taɓawa, sannan an hana dukkan Amurkawa yin mu’amalar kuɗi da ASG. Bugu da ƙari, laifi ne mutum ya samar ko ya yi yunƙurin samarwa ko ya taimaka wajen samar wa ASG kayan aiki da gangan.
