Labaran da suka tabbata

Toting Craft Hanno (Ɗaurarre)

Garkuwa da Amurkawa da kuma kashe su a Philippines 

RFJ ya biya ladan dalar Amurka 100,000 don bayanan da aka bayar da suka kai ga kama shugaban ‘yan ta’addan ƙungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group – ASG) mai suna Toting Hanno a Philipphines. 

Toting Craft Hanno mamban ASG ne da ke da hannu wajen yin garkuwa da Amurkawa a ranar 27 ga watan Mayun 2001 daga Tsibirin Dos Palmas a Palawan a Philippines. Amurkawan uku su ne Guillermo Sobero, da ma’aurata kuma ‘yan mishan Martin, da Gracia Burnham. A ranar 11 ga watan Yunin 2001, kakakin ASG Abu Sabaya ya sanar da cewa na kashe Guillermo Sobero a matsayin “kyautar ranar haihuwa” ga ShugabanPhilippines Gloria Macapagal-Arroyo. A ranar 7 ga watan Oktoban 2001, an gano wani ƙoƙon kan mutum a Tsibirin Basilan, wanda aka tabbatar cewa na Guillermo Sobero ne. A watan Yunin 2002, Martin Burnham ya mutu yayin musayar wuta tsakanin sojojin Philipphines da na ASG; an raunata Gracia Burnham amma an ceto ta kuma aka mayar da ita Amurka.

A ranar 6 ga watan Janairun 2005, jami’an tsaron Philipphines, bisa bayanan sirri da aka ba su, suka kama Hanno.

Skip to content