Labaran da suka tabbata

Abu Solaiman (Wanda ya mutu)

Garkuwa da Amurkawa da kuma kashe su a Philippines

RFJ ya biya ladan dalar Amurka miliyan biyar ga mutum biyu da suka bada bayani kan shugaban ƙungiyar Abu Sayyaf (Abu Sayyaf Group – ASG) Abu Solaiman. A ranar 7 ga watan Yuni na 2007, jakadan Amurka a Philippines ya jagoranci biyan ladar ga mutanen a wajen wani biki a bainar jama’a da ya gudana a tsibirin Jolo.

Abu Solaiman na cikin manyan shugabannin ASG, ƙungiyar ta’addancin da ke aikin ta’addanci a Philipphines. Solaiman da Khadaffy Janjalani na da hannu a sacewa da kuma kisan ‘yan ƙasashen Philippines da Amurka. An gano Solaiman na da hannu a garkuwa da Martin da Gracia Burnham da wasu Amurkawa biyu, sannan yana da hannu a sare kan ɗan Amurka Guillermo Sobero. Kazalika, Solaiman ya shirya tare da aiwatar da hare-hare a kan kadarorin Amurka kamar dasa bam a Ofishin Jakadancin Amurka da ke Manila, da nitsar da jirgin Superferry 14 a Fabarairun 2004, da dasa bama-bamai uku a Ranar Masoya wato Venlentine’s Day ta 2005, wanda jimilla ya kashe ko jikkata ɗaruruwan fararen hula.

A ranar 16 ga Fabarairun 2007, Rundunar Sojan Philippines, bisa bayanan sirrin da masu bada bayanai suka bayar, suka ƙaddamar da harin kama Solaiman. Solaiman ya yi tsayayya a lokacin harin amma an kashe shi.  

Skip to content